Ruguntsimin Babbar Sallah

0

A yau Lahadi aka shiga rana ta uku ana ci gaba da gudanar da shagulgulan Babbar Sallah a fadin kasar nan. Ga tsakuren wasu labarai da su ka gudanar a ranar farko da kuma Asabar washegarin Sallah.

EKITI: Gwamna Fayose ya kwashe daruruwan ‘yan kallo jim kadan bayan kammala Sallar Idi a babban filin Idin Ado-Ekiti. Bayan kammala Sallah, Fayose wanda mabiyin addinin Kirista ne, ya tara manyan malamai a Masallacin Idi tare da dimbin al’ummar musulmi.

An nuno shi ya na wa’azi, inda ya ke kiran da a zauna lafiya da juna, Najeriya daya ce, ba a bukatar ta tarwatse. Daga nan kuma ya yi jawabi mai tsawo, inda ya gargadi jama’a a daina kwacen matan mutane.

DAURA: A jiya Asabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dan Najeriya zai iya zama a ko’ina cikin kasar nan ya yi rayuwar sa. Ya yi wannan furuci ne yayin da ya karbi bakuncin Gwamnan Katsina, Aminu Masari, a Daura.

KANO: Ranar Asabar ne kuma a Kano da yamma, ‘yan sara-suka da ake zaton mabiya wasu manyan yan siyasar Kano ne suka yi wa juna jina jina.

Wannan hari dai ya afku ne a lokacin Hawan Daushe. An sassari wasu da dama da adduna da takubba. Wasu kuma an sossoke su da wukake.

KATSINA: A Katsina kuma an wayi garin Asabar birnin ya cika da fastocin takarar shugaban kasa mai dauke da hoton Gwamnan Jihar Zamfara, Abubakar Yari. Ba a dai san ko su wa ke da alhakin bugawa da lika fastocin a Katsina ba.

BAUCHI: ‘Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta bada sanarwar kama wasu mutane masu yanke wa mutum hukuncin kisa, ba tare da an mika shi hannun hukuma ba.

Kungiyar dai ana kiran ta da suna Ba-beli.

KANO: Har ila yau a Kano. Asabar da dare an ji karar fashewar wani Abu mai kara. Wasu kuma sun ce rurin harbin bindiga ne. Sai dai kuma an ruwaito cewa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce kowa ya kwantar da hankalin sa, babu wata barazana tashin hankali a jihar.

KADUNA: Zuwa yau Lahadi dai garin Kaduna Shiru, komai salin-alin. Daga kanshin suya sai ba babban kawai kaji. Mahaya kuwa da masu sarauta sun yi garin Zazzau domin hawan Daushe da za ayi.

Share.

game da Author