Kamar yadda aka sani ne cewa fannin kiwon lafiya a Najeriya na fama da matsaloli da dama wanda hakan ke hana mutanen kasar samun ingantacciyar kiwon lafiya.
Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya ta ce mafi yawa yawan yara a kasar na mutuwa kafin su cika shekara biyar sanadiyyar kamuwa da cututtuka kamar su tarin lala, kenda, sankarau, shan inna da sauran su.
Hukumar ta ce karancin kudin da fannin kiwon lafiya ke fama dashi ne babban matsalar da ke ci wa fannin tuwo a kwarya.
Hukumar ta ce sanadiyar haka;
1. Yara 128 daga cikin 1000 ‘yan kasa da shekara biyar ke rasa rayukansu a kowace shekara.
2. Bincike ya nuna cewa kashi 34.5 bisa 100 na yara yan kasa da shekara biyar da ke dauke da cutar sanyi wato ‘Pneumonia’ ke iya samun magani a asibitoci.
3. Kashi 36.5 bisa 100 na yara kanana wanda ke kamuwa da cutar da ake samu ta hanyar shakar gurbataciyyar iska ne kadai ke samun maganin cutar.
4. Kashi 38.1 bisa 100 na yara kanana kadai ke samun maganin cutar amai da zawo.
Discussion about this post