Osinbajo ya nisata kansa da masu yi masa kamfen din fitowa takarar Shugaban kasa

0

Mataimakin Shugaban Kasa Yesmi Osinbajo ya nisanta kan sa daga wani kamfen da aka fara yi cewa ya cancanci fitowa takarar shugabancin kasar nan a 2019.

Wata kungiya ce dai da ba ta fito karara ta bayyana kan ta ba, ita ce ta fara yayata wannan kamfen a kafafen sada zumunta a yanar gizo. Sai dai kawai ya ce tushe da hedikwatar kungiyar na can a birnin Belfast, babban birnin kasar Ireland ta Arewa.

Kakakin Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande ne ya nisanta Osinbajo daga wannan kungiya, ya na mai cewa makaryata ne . Ya ce Mataimakin Shugaban Kasa bai taba nunawa ko furtawa cewa zai tsaya takara ba.

Akande ya ce Osinbajo mutum ne mai biyayya ga gwamnati, jam’iyya da kuma shugaba Muhammadu Buhari. Hasali kuma bai ma san da wata kungiya na yi masa kamfen ba.

A karshe ya roki jama’a su yi watsi da kamfen din domin ba da yawun Osinbajo su ke yi ba.

Share.

game da Author