Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya soki yanayin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke gudanar da aikin sa, ya na mai cewa shugaban ya na tafiyar hawainiya ko kuma ba ya hanzari wajen cika alkawurran da ya dauka a lokacin zabe.
Obasanjo ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da mujamllar ‘African Arguments’ ta yi da shi. Ya na mai cewa Buhari bai tabuka abin a zo a gani ba, musamman wajen samar da ayyukan yi ga dimbin matasan kasar nan.
“Dukkan matasan Najeriya su na da dalili da hujjar hasala da jin haushin wannan gwamnatin. E, na san Buhari ya tabuka a wasu fannonin. Ya yi kokari wajen harkar noma, amma abin bai isa ba fa. Abin da ya yi bai kai abin da za mu iya bugun gaba mu ce mun fita daga matsalolin ko mun kamo hanyar inganta tattalin arzikin kasa ba.”
Ya ce Shugaban Kasa zai iya kokartawa wajen tallafa wa matasa, sannan kuma ya ce idan aka tallafa wa matasan da aikin yi, koyon sana’o’in hannu da kuma ilmi, to za a samu saukin hayagaga da hauragiyar tayar da zaune tsaye da matasa ke yi a kasar nan.
Dangane da masu neman kafa Biafra, Obasanjo ya ce wadannan gafalallu ne, ba ma san abin da su ke yi ba.
Dangane da yawan tsangwamar sa da ake yi wai kafin ya zama shugaban kasa, naira 20,000 ce kacal a cikin aljihun sa, amma bayan ya zama shugaba sai ga shi ya zama daya daga cikin manyan attajiran Afrika, Obasanjo ya ce wannan sharri ne da karya aka kitsa masa.
Ya ce kafin ya zamo shugaban kasa shi ba matsiyaci ba ne, domin a lokacin shi ne ke da gidan gonar kiwon kaji mafi girma a fadin Afrika.
A karshe ya ce masu so a canja fasalin Najeriya ‘yan ragabza da giribtu ne kawai. “Wane irin karfin iko ne gwamna ba shi da shi a yanzu. Akwai gwamnonin da sun ma fi shugaban kasa iko a jihohin su.”
Discussion about this post