Shugaban kungiyar Biafra Nnamdi Kanu ya kalubalanci hukuncin da kotu a Abuja ta yanke na ayyana kungiyar IPOB ‘yan ta’addanci.
Nnamdi Kanu ya fadi haka ne ta bakin lauyansa Ifeanyi Ejiofor ranar Juma’a.
Ifeanyi Ejiofor ya ce hukuncin da babbar kotun kara ta yanke ranar 21 ga watan Satumba bai kamata ba domin ta yi hakan ne ba tare da ta ji daga bangarensu ba.
Ya ce kamata ya yi ta ji daga bakin shugaban kungiyar Nnamdi Kanu (wanda ya cika wa wandonsa iska tun da aka fara rikicin makonni biyu da suka wuce) kafin ta yanke hukunci.