Nnamdi Kanu: Dalilan da ya sa muka yi harbi sama a garin Umuahia – Rundunar Sojin Najeriya

1

Rundunar Sojin Najeriya ta Karyata labaran da ake ta yayadawa a kafafen yada labarai cewa wai sun kai hari gidan Nnamdi Kanu a garin Umuahia, jihar Abia.

Rundunar Sojin ta ce duka abin da ake ta yadawa ba haka bane, domin gaskiyar maganan shine, rukunin Soji na 14 na wani atisayi a jihar inda samari masu tattakin nuna goyon baya ga kungiyar IPOB suka tare hanya wai sojojin ba za su wuce ba.

Daga nan ne fa suka fara jifar motocin Sojojin inda har suka ji ma wani soja mai suna Kolawole Mathew ciwo da wata mata mai wucewa.

Dalilin haka ne Sojojin suka bude wuta suna harbin sama don su tarwatsa dandazon matasan.

” Babu wani rai da aka rasa a wannan yamutsi.” Inji kakakin rukunin Sojin na 14, Oyegoke Gbadamosi.

Share.

game da Author