Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya bayyana cewa ana bukatar karin ‘yan sanda a kasar nan har 31,000 a kowace shekara har tsawon shekara biyar.
Ya ce hakan ne kawai zai sa Najeriya ta kai daidai sharuddan da majalisar dinkin duniya ta gindaya cewa kowace kasa ta samar da dan sanda daga mutane 400.
Sai dai kuma sifeto Janar din cewa ya yi a yanzu Najeriya na da dan sanda daya a kan mutane 600. Sai ya kara da cewa, matsawar ana so a cimma samar da ‘yan sanda 1 a kowane jama’a 400, to hakan zai tabbata.
A taron dai an yaye dalibai1,150 a Kwalejin Horon ‘Yan Sanda yau Juma’a a Kaduna.
Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ya dauki ‘yan sanda su dubu 11,000 a cikin 2017.
Daga nan sai ya ja kunnen daliban da aka yaye daga kwalejin da su guji dukkan wata ribbata, cin hanci da duk wani abu da zai zubar da kimar su.