Musulunci da wuya, na yi wa miji karya ne a zaman auren mu shekaru 19, amma ni Coci nike zuwa – Taofeekat

0

Wata mata mai suna Taofeekat ta sanar wa Kotu cewa ta ki yin addinin musulunci ne bayan ta ga ba zata iya hakan aikata ayyukan da addinin ya shar’anta ba.

Ta ce ta kan boye ta tafi cocin ta tsawon shekaru 19 da sukayi da mijinta na aure.

Mijin ya nemi kotu da ta warware wannan aure nasu saboda bayan ya gane cewa bata iya karanta komai daga cin Alkur’ani ba sannan bata sallah.

Kotu ta amince wa mijin nata hakan sai dai ta amince masa da ya dauki ya’ya biyu cikin ukun da suka Haifa sannann dayan da za a bar mata zai ci zai dinga biyan kudin ciyarwa duk wata naira 4000.

Share.

game da Author