Muna cikin halin ha-u-la-i a zaman da muke yi a sansanonin ‘yan gudun Hijira

0

Wata kungiya mai zaman kanta ‘Bama Initiative for Human Development’ tare da wasu ‘yan gudun hijira a jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga domin nuna gajiyarsu da zama a sansanonin yan gudun hijira da ke jihar.

Shugaban kungiyar Muhammad Hassan yace ‘yan gudun hijiran sun kagara su koma garuruwansu ganin cewa zaman lafiya ya dawo a garuruwan.

Muhammad Hassan yace halin rayuwar da ‘yan gudun hijira a sansanonin ke fama da shi yasa dole ko ka ki Allah ka tausaya musu.

“Ba ma iya tafiyar ta rayuwar mu yadda ya kamata, yaran mu basa zuwa makaranta sannan yunwa sai kashe mu ya ke yi.”

‘Yan sanda sun dakatar da zanga-zanga in bayan haka gwamnan jihar Kashim Shetima ya yi kira ga mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira da su mara wa gwamnatin jihar baya kan kokarin da takeyi na gyara garurun da Boko Haram ta lalata.

Kakakin gwamnan Jihar, Isa Gusau ya ce gwamantin jihar ta gina makarantu, Gidajen zama, Asibitoci, Kasuwani da ofisoshin ‘yan sanda a kananan hukumomi 15 a jihar.

Ya kara da cewa gwamantin na horar da ma’aikatan da za su samar da tsaro a jihar wanda za su kare rayuka da dukiyoyin mutane bayan sun komo garuruwan nasu.

Daga karshe Isa Gusau ya ce gwamanti na kokarin ganin cewa ta gyara komai yadda ya kamata kafin ta bar ‘yan gudun hijira su fara komawa garuruwansu.

Share.

game da Author