Mazauna kauyen Maiyola dake karamar hukumar Kajuru jihar Kaduna sun koka kan rashin asibiti da suke fama da shi a kauyen.
Yan kauyen sun ce dalilin haka kusan duk wata sai an rasa mace mai haihuwa ko kuma yaro.
Salamatu Haruna mazauniyar kauyen ta ce saboda rashin asibiti a kauyen mafi yawa yawan mata masu ciki basa samun kulan da ya kamata lokacin da suke da ciki musamman wajen awo.
Ta ce ‘‘Sai dai mu taka zuwa asibitin Kachia ko kuma Idoh wanda nisan su ya kai kilo mita 100 kafin muke samun kula”
” Koda nakudar haihuwa ta kama mace misali da daddare sai dai mu nemi unguwar zoma na gargajiyya don rashin ababen hawa sanadiyyar lalacewan hanyoyin mu.”
Hafsat Abubakar da Zainab Abubakar sun ce su kan ziyarci shago da ake siyyar da magugunan ko kuma su yi amfani da maganin gargajiyya a duk lokacin da suka fara laulayin ciki
Ita kuwa Maryam Maiyola mai shekaru 60 ta ce yawan farashin kudin asibiti na cikin matsalolin da matan kauyen ke fama da su.
Ta ce sau daya ta taba samun yin awon ciki a asibiti inda ta biya kudade da dama domin samun kulan da take bukata.
‘‘Na biya kudade da yawa lokacin da na je asibiti domin likitocin sun ce naje na yi hoton cikin’’.
Wani magidanci Mohammed Adamu ya koka kan wahalhalun da mata masu ciki ke fama da su a kauyen.
Ya ce ya rasa matarsa tare da dan dake cikin ta lokacin da suke hanyar zuwa asibiti.
Ya kara da cewa tun da suke zama a kauyen Maiyola babu wani dan jarida da ya taba zuwa don ruwaito halin da suke ciki a kauyen.
“Muna murna da wannan ziyaran da kuka kawo mana.”
Daga karshe mai unguwan Maiyola Ardo Abu Maiyola yace ‘‘Ran mu na matukar tashi a duk lokacin da matan mu ke da ciki. Ikon Allah ne kawai ke rayar da mu a wannan kauyen.
Ya ce kauyen ta kai shekaru 40 da kafa ta amma basu taba samun ko da cibiyar kiwon lafiya ba ne.