MUGUWAR KISHIYA: Amarya ta jefa ‘ya’yan kishiya biyu rijiya

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa ta bayar da sanarwar cewa sun kama wata matar aure mai suna Aisha Isah, a bisa zargin ta da laifin jefa yara biyu, dukkan su ‘ya’yan kishiyar ta a cikin rijiya.

Aisha ta jefa Zainab mai shekara hudu da kuma Baba dan shekara biyu cikin rijiya, bayan ta yi wata kazamar tankiya da uwar su.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Kennedy Idrisu ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labarai wannan labari a Lafiya, babban birnin jihar.

Ya kara da cewa an cafke wadda ake zargin a kauyen Yelwan-Bassa, cikin Karamar Hukumar Kokona.

Ya kuma ce wadda ake zargin ta amsa laifin ta, kuma ta na cikin nadamar aikata hakan.

Idirisu ya kara da cewa, binciken ’yan sanda ya nuna Aisha, wadda ita ce amaryar Alhaji Isah, a kullum ta na cikin rigima da uwargidan ta, Maimuna. Duk wani kokari da mijin ya sha yi domin ya sulhunta su, bai yi nasara ba.

Ita dai ta yi ikirarin cewa uwargidan wato Maimuna, ta sha tsokanar ta tare da zuga ‘ya’yan ta cewa ko ta kira su domin ta aike su, to kada su sake su je. Wannan ne ya fara kuntata Zainab rai, kasancewa ba ta da da ko daya.

Aisha ta taba haihuwar ‘ya mace a cikin 2016, amma ta mutu bayan watanni shida da haihuwar ta. Ta ce ta jefa Baaba a cikin rijiya a cikin watan Afrilu, 2017, amma tunda babu wanda ya ga lokacin da hakan ta faru, sai kowa ya kaddara cewa tsautsayi ne kawai.

‘Yan sanda sun ce a ranar 26 Ga Agusta kuma, sai Aisha ta kwartsa ihun neman gudummawa, wai ga Zainab can ta fada rijiya. Nan take mijin ya garzayo domin ya tsamo yarinyar.

Mijin ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya tsamo Zainab babu rai, kuma abin al’ajabi, sai ya ga hannayen ta biyu a daure. Wannan ne ya sa aka fara zargin Aisha, har aka kama ta.

Daga baya Aisha ta amsa laifin ta, kuma ta ce ita ce ta tura Baaba rijiya can baya a cikin watan Afrilu.

Kakakin ‘yan sandan dai ya ce da zaran sun kamfala bincke, za su yi gaggawar iza keyar ta kotu domin yi mata hukunci da ya yi daidai da abin da ta aikata.

Share.

game da Author