Mu yi kokarin kauce wa barkewar wani yakin Basasa -Shugaban Kiristocin Najeriya

0

Shugaban Kungiyar Kiristocin Kasar nan, CAN, ya yi kira da a hada kai da juna domin tabbatar da an kauce wa barkewar wani yakin Basasa a kasar nan.

A cikin sakon sa na taya murnar bukin babban Sallah ga daukacin musulmin kasar nan, Samuel Ayokunle ya ce a tarihin duniya ba a taba samun kasar da aka yi yakin basasa sau biyu ba ta tarwatse ba.

Sai ya sake Jan hankalin Musulmi da su ci gaba da nuna halin takawa da tsoron Allah kamar yadda Annabi Muhammadu (SAW) ya yi, kuma ya koyar da a yi.

Takardar sakon wadda jami’in yada labaran sa Bayo Oladeji ya sa wa hannu, ya ce gwamnatin Najeriya da daukacin al’ummar kasar nan na da nauyin da ya rataya a kansu domin kauce wa duk wani abu da zai ta da zaune tsaye.

“Lokacin ya yi da gwamnatocin kananan hukumomi, jihohi da tarayya za su kara himmar rage radadin talaucin da ke damun mutane.

” A matsayin Musulmi masu bikin murnar sallah domin tuna yadda Annabi Ibrahim (AS) ya bi umarnin Allah (SWT), ya na da kyau a tunatar wa Musulmi fadar Allah a cikin Alqur’ani: “Ba nama ko jinin dabbar da aka yanka ke isa ga Allah ba. Allah na dubi ne da tsoron sa da imanin da ke cikin zukatan ku.”

A karshe shugaban na CAN ya ja hankalin ‘yan siyasa da su cika alkawurran da su ka daukar wa talakawan da su ka zabe su.

Share.

game da Author