Hukumar Hana Cin Rashawa da Zambar Kudade, EFCC, ta fara shirye-shiryen ganin an kamo tsohuwar ministar man fetur ta lokacin muklin Goodluck Jonathan, Madam Diezani Maduekwe domin a hukunta ta.
Dimbin ‘yan Nijeriya na ta faman kiraye-kirayen a dawo da ita Nijeriya daga Ingila, domin ta fuskancin zargin wawurar makudan kudaden da ake yi mata.
Gwamnatin Tarayya dai ta kwace kadarori na bilyoyin nairori da aka danganta su da cewa duk na ta ne.
Da ya ke magana jiya Laraba yayin wani jawabi ga ‘yan jarida da kungiyoyin sa kai, Shugaban EFCC na riko, Ibrahim Magu, ya tabbatar da cewa sun a kokarin ganin an kamo tsohuwar ministar daga Ingila inda ta ke a makale.
“Ina so na kara jaddada mu ku cewa duk wanda aka kama da laifi to fa sai an hukunta shi. Domin mu na kokarin ganin an dawo da Diezani gida Nijeriya domin a hukunta ta. Amma har yanzu mu na ci gaba da bincike.”
“Mun rigaya mun kai matakin da babu wanda ya isa ya hana mu wannan yaki da zambar kudaden da cin hanci, amma tilas sai dukkannin mu mu yarda cewa mu na da ruwa da tsaki sosai wajen wannan yaki. Domin yaki ne domin gyara rayuwar mu da ta wadanda za su biyo bayan mu.”
Magu ya kuma ce ita fa EFCC za yi bakin nata kokarin, ya kamata jama’a su tashi su bayar da gudummawa, ita ma doka ta rika yin aikin ta, ta hanyar gaggauta yanke hukunci ga mabarnatan dukiyar kasar nan.
A karshe ya danganta dukkan wani hankoro da hayagagar neman ballewa ko an danne wani yanki da cewa duk alamomin yadda cin hanci ya yi kaka-gida ne a kasar nan. Hatta yawan yajin aiki ma, Magu ya ce duk musabbaban su rashawa da cin hanci ne.
“Ina rokon duk wani mai zargin akwai masu yin harkalla a EFCC da ya fito ya kawo mana shaidu, mu kuma za mu dauki kwakkwaran mataki. Domin idan akwai harkalla a cikin hukumar hana harkalla, ai an yi ba a yi ba kenan.” Inji Magu.
Discussion about this post