Wasu mazauna Abuja, Babban Birnin Tarayya, sun fara kokawa da kuma nuna mamaki da al’ajabi, ganin yadda ake yawan samun mazaje masu shigar mata da kwaikwayon rayuwar su a kasar nan.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ruwaito cewa an kama wasu matasa wadanda su ka yi shigar mata, su ka damfari wasu mutane a Lagos, Zamfara, Rivers da Abuja, ta hanyar yin shigar mata.
Wata mai harkar kayan kwalliya da shafe-shafe mai suna Joy Nduka, ta ce ta na mamakin yadda yanzu a kasar nan, kamar ya amince da masu irin wannan shiga, ana ganin ba ta da wata illa a koyarwar da’a da zamantakewar mu.
“Sau da yawa za ka ji an damfari maza ta hanyar yin shigar mata. Amma abin mamaki a ko da yaushe ba a maida hankali wurin wadanda ke damfara, sai dai wadanda aka yi wa damfarar.
“Ina kuma mamakin yadda maza ke saurin fadawa tarkon masu shigar mata su yi musu damfara. To sai na yi nazari, na ga ma ba a ankara da illar masu shigar mata za su iya haifar wa a cikin al’umma.”
Ita ma Itamunoala cewa ta yi, da farko Denrele ta sani wanda ke fitowa a wasu shirye-shiryen ‘yan kwalisa a talbijin. Ta ce abin mamaki kuma duk harkar da ya tsoma kafa ko hannun sa, in dai ta kwalisar mata ce, to sai a ga ya na samun nasibi.
Itamunoala ta ce hakan na nufin fa al’aumma ta kau da kai daga ganin irin aibin wannan dabi’ar kwaikwayon kayan mata da ya zama ruwan dare maza na yi a yanzu.
“A baya ‘yan Nijeriya na kyamar masu irin shigar ‘yan daudu. Amma a yau abin ya mamaye kasar nan. Ku dubi irin su Snapchat queen da Bobrisky wadanda tauraron su ke haskawa a shafunan yada zumunta, ‘soshiyal midiya’.”
Sunan Bobrisky na ainihi dai Okuneye Idris, amma da rana tsaka ya rikide ya na shigar mata, ya canja suna zuwa Bobrisky.
“Borisky din nan fa a da bakin kato ne wulik, amma a yanzu ya yi shafe-shafe ya fatar sa ta koma fari. Ba ya komai sai kwaikwayon mata, ya na yawo cikin duniya ya na samun makudan kudade. ‘Yan Nijeriya kuma har turereniyar daukar hoto ake yi da shi, ana ba shi kudi.”
Ta ce ana wannan irin rayuwa amma al’umma ta kau da kan ta, idan ba a yi aune ba, ku na nan a Nijeriya za a lasata auren jinsin mace da mace, ko namiji da namiji.
Discussion about this post