Matsayar Sarakuna da Malaman addini kan tsarin Iyali

0

Taron da Ma’aikatar Lafiya ta Kasa ta shirya tare da hadin guiwar Gidauniyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yawan al’umma da kuma wasu kungiyoyi daban, ya samu halartar Sarakunan Gargajiya da malaman addini.

Da ya ke jawabi a Dakin Taro na Transcop Hilton hotel, Abuja, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ya jaddada cewa matukar ana so a kai ga biyan bukatar shirin tsarin iyali a kasar nan, tilas sai an sake sabon lalen hanyar isar da sako da wayar da kan jama’a tukunna.

Sultan, wanda Mai Martaba Sarkin Shongha, Haliru Yahaya ya wakilta, ya ce a gaskiya an zuguguta batun tsarin iyali da yawa, don haka sai an sauko daidai da tunanin na kasa ta hanyar isar da sako na kai-tsaye ga al’umma.

Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su karbi shirin tsarin iyali hannu biyu, ya na mai cewa, “Musulunci ba ya kyamar sabbin dabarun zamani, kuma tsarin iyali na daya daga cikin wannan ci gaban fasaha na zamani wanda zai iya taimaka wa rayuwar al’umma da kuma ingata lafiyar su.

” Duk da cewa akwai abubuwan da Musulunci ya yi hani da kuma kwadaitarwa a yi dangane da tsarin iyali, Sarkin Musulmi ya yi kokarin ganin ya kwadaitar da malaman Musulunci da yin duba da nazarin inda tsarin iyali ya kauce wa ka’idar Musulunci, musamman a batun takaita yawan al’umma.

“Mun zo da wani littafi mai suna: ” Tsarin Iyali a Mahangar Musulunci a Nijeriya” kuma mu na yin kira ga dukkan malamai da su amshe shi hannu biyu, su koyar da shi, saboda ya fi kusanci da fahimtar mutanen karkara.”

Shi kuwa Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, kira ya yi ga gwamnati da ta bai wa tsarin iyali matukar muhimmanci. Ya ce irin yadda ake samun yawaitar mutuwar mata masu juna biyu a wurin haihuwa, abu ne mai tayar da hankali. Sai dai kuma a ta bakin sa, a kasafai ake kula da hakan ba, saboda abin ne da yawa, wai mutuwa ta shiga kasuwa.

Ya ce lokaci ya yi da za a fito haikan a yi wa jama’a kamfen din yin tazarar iyali, domin kauce wa yawan daukar cikin da ba a tsammani.

“A kullum akalla ana samun mata 110 na mutuwa yayin haihuwa a kasar nan. Haka nan mutuwar jirajirai ma babbar asara ce a kasar nan. Ya kamata mu dauki tsarin nan da muhimmanci. Ba abin da kawai za mu tattauna a nan, mu tashi kawai ba ne. Nauyi ne da ya rataya a kan kowa a kasar nan.”

Shi kuwa mai wakiltar Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN, Jonah Johnson, cewa ya yi gwamnati ta fito ya yi Abu a aikace ta rage babatu. Tsarin iyali ba babatu kadai ba, sai fa an fito an aiwatar sannan za a samu nasara.

Ya jaddada cewa kungiyar CAN za ta ci gaba da goyon bayan shirin tsarin iyali a kasar nan.

Share.

game da Author