Wani fasto ya roki kuto ta warware aurensa da matarsa saboda tsine masa da takeyi da tsiraicinsa.
Bernard Towoju wanda fasto ne ya ce mai dakin sa ba ta da mutunci ko kadan.
” Duk lokacin da wani abu ya hada mu da ita sai ta tube tsirara tana tsine min. Kuma na gaji da wannan abu da take yi.
” Ta taba zuwa ofis dina ta yayyaga mini kaya ta na zafi na. Sai da abokan aiki na su ka taimaka mini.
” Idan masifarta ko tsiyarta ya tashi, har da kwalabe, gatari da sanduna zaka ga tana bina.
Ya roki kotu ta raba auren su Kafin ta kashe shi.
Matar Benerd ta roki kotu da kada ta raba aurenta da mijin ta domin tana matukar sonsa.
Kotun ta daga ci gaba da sauraren karan zuwa watan gobe.
Discussion about this post