Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha mallakar gwamnatin tarayya dake Kaduna, Kaduna Polytechnic ta shiga yajin aiki daga yau Juma’a, 8 ga watan Satumba.
Jami’in kula da harka da jama’a na kungiyar Abass Muhammed ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya haka a hira da yi da su ta wayan tarho.
Ya ce kungiyar ASUP reshen Kwalejin Kaduna ta shiga yajin aikin ne don rashin biyan tarin bukatunsu da hukumar makarantan ta kasa biya.
Idan ba a manta ba kungiyar ASUP a ranar 18 ga watan Yuli ta dakatar da yajin aikin da ta fara yi bayan ta tattauna da hukumar kwalejin kan biyan bukatun malaman sannna bada da watanni uku domin hakan su biya musu bukatun.
Ya ce bukatun nasu sun hada da;
1. Rashin biyan wasu alawus din malamai
2. Rashin kayayyakin aiki na koyarwa ga dalibai.
3. karanci ofisoshi da kujerun zama.
4. Rashin gyara gine-ginen da ke kwalejin.
5. Karancin bandaki.
6. Rashin wuraren shakatawa da wasanni.
Daga karshe kungiyar ASUP ta ce tana kira ga gwamnati, masu ruwa da tsaki da mutanen kasa da su taimaka wajen jawo hankalin hukumar makarantar ta biya musu wadannan bukatu.
Discussion about this post