Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi, ya ce babu wani sabani tsakanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da kuma Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickon.
Shi ma Jonathan ya karyata wannan jita-jitar cewa wai ya na kokarin kankane jam’iyyar a jihar, ya na mai cewa rudu da shaci-fadi ne kawai.
Makarfi ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke karbar bakuncin ‘yan kwamitin zartaswar jam’iyyar na jihar Bayelsa, bisa jagorancin shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Cleopas Moses, a sakatariyar jam’iyyar, a Abuja.
Makarfi ya kara da cewa, yayin da aka fara baza wannan ji-ta-ji-tar, Jonathan ya kira shi ya ce duk karya ce, ba shi da wata matsala da Seriake, gwamnan na Bayelsa, jihar da Jonathan ya fito.
Ya kara nanata cewa shi kan sa ya na yin waya da Jonathan da kuma gwamna Dickson, inda ya ke kara tabbatar da cewa babu sabani a tsakanin su.
Ya dai gano cewa akwai wasu munafukai da algungumai wadanda ke neman haddasa rashin jituwa a cikin jam’iyyar ta jihar Bayelsa.
“Ina kira gare ku, kada ku bari haka kawai masu kirkirar karya da sharri su karya ku ta yadda hadin kan ku zai raunana. Batun yada karya wai ana shirin rushe kwamitin zartaswa na jihar duk zancen banza ne kawai na munafukai.
PREMIUM TIMES HAUSA ta yi nazarin cewa ba abin mamaki ba ne idan har aka samu sabani tsakanin Jonathan da Dickson, domin ba shi ne karon farko da aka fara samun irin haka tsakanin yaro da ubangidan siyasa ba, musamman wadanda su ka taka matsayi na gwamna ko na shugabancin kasa da su ka fito a jiha daya.
An sami irin wadannan rade-radi tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa a zamanin mulkin Jonathan, Namadi Sambo da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna na lokacin, Ramalan Yero.
Irin wannan sabani da rashin jituwa ta janyo musu janyewar mabiya siyasar su. Rahotanni sun ce baya ga nisantar juna da Namadi ya yi tare da Yero, su biyun sun wayi gari an watse an bar su, tun bayan faduwa zaben da su ka yi a 2015.
Kada kuma a manta, a jihar Zamfara, Sanata Ahmed Yerima ya sauka daga mulki ya bai wa mataimakain sa takara. Wanda kuma shi ne na farko da ya fara amince wa mataimakinsa ya tsaya takara bayan shi a kasar nan.
Mataimakin nasa Aliyu Shinkafi, bai dade da cin zabe ba, sai ya koma jam’iyyar PDP. Wannan kuwa ya kawo mummunan sabani a tsakanin su.
Sanata Yerima ya yi kokarin hada kan mabiyan san a siyasa, domin hana Shinkafi zarcewa, inda ya tsaida daya yaron sa, Abdul’aziz Yari, ya yi nasara akan Shinkafi.
Wani kazamin sabani da ya fi fitowa fili a yanzu, shi ne tsakanin Sanata Rabi’u Kwankwaso da Gwaman Abdullahi Ganduje na jihar Kano. Ganduje ya yi wa Kwankwaso mataimaki tsakanin 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015.
Bayan samun nasara a karkashinn jam’iyyar APC a zaben 2015, an yi tunanin kyakkyawan zumunci zai dore tsakanin manyan ‘yan siyasar su biyu.
Sai dai kuma tun tafiya ba ta yi nisa ba, aka yi mummunar batawar da a yanzu ta kai Ganduje da Kwankwaso ba zu cin tuwo akushi daya, kuma ba su iya zama a cikin inuwa daya.
Su kan su magoya bayan su, banda rikici, husuma da yarfe, har ta kai su ga mummunan fada a lokacin bikin Babbar Sallar da ta gabata a Kano.
Dalili kenan wasu ke ganin cewa ba abin mamaki ba ne idan sabani ya shiga tsakanin Jonathan da Dickson, wanda a farkon shigowar sa gwamnatin Jonathan, ya fara da mukamin karamin minstan ilmi bayan zaben 2011. Dickon ya yi aiki tare da babbar ministar ilmi ta lokacin, Farfesa Ruqayyatu.
Daga bisani Dickon ya tsaya takarar gwamnan Bayelsa, ya yi nasara.
Ganin cewa a yanzu mulkin Najeriya ya subuce daga hannun Jonathan, zai nemi tudun dafawa domin samun jama’ar da za su kare masa mutunci ko da a siyasar jihar sa ne.