Mahajjata biyu daga jihar Katsina sun rasu a Makka

0

Shugaban hukumar kula da walwalan mahajjata na jihar Katsina SPWA Salisu Shinkafi ya ce mahajjata biyu da ga jihar sun rasa rayukansu a kasar Saudi.

Ya sanar da hakan a lokacin da yake zantarwa da manema labarai a Makkah ranar Talata.

Salisu Shinkafi yace sunyi jana’izan mamatan wanda ya hada da mace daya da namiji daya bayan sun kammala yi musu sallah a masallacin Makkah.

Ya kuma kara da cewa mahajjata 1,776 daga cikin 4776 da suka zo aikin haji daga jihar Katsina sun dawo Najeriya.

Ya ce sauran mahajjata 3000 na cikin koshin lafiya sannan za a dawo da su kasa Najeriya nan da ranar 28 ga watan Satumba.

Salisu Shinkafi ya ce gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya kara wa mahajjatan jihar riyal 300 sannan ya yi kira ga mahajjatan da su ci gaba da yi wa kansu da iyalensu, jihar Katsina da Najeria musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari adu’a.

Share.

game da Author