Likitocin Najeriya sun fara yajin akin gama gari

0

Kungiyar likitocin Najeriya NARD ta sanar da fara yajin akin gama gari da likitoci suka shiga daga ranar Litini a fadin kasar.

Shugaban kungiyar Onyebueze John ya sanar da haka ranar Litini bayan kammala taron tattaunawan da mambobinta da kungiyar ta yi wanda suka fara daga karfe 7 na yammacin Lahadi zuwa 3 na asubahin Litini.

Ya ce sun yarda su fara yajin aiki na gama gari ne bayan kin cika alkawurran da gwamnati ta dauka na inganta aikin su.

Ministan kwadugo Chris Ingige ya sanar ranar Lahadi cewa kungiyar ta amince da janye wannan shiri na ta inda a bisani kungiyar ta fito ta Karyata haka.

Asibitocin koyarwa da ke karkashin jami’oin kasarnan da wasu manyan asibitocin kasa ne za su kasance kulle har sai an gano bakin zaren tsakanin gwamnati da kungiyar ma’aikatan.

Share.

game da Author