Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya ta doke takwararta ta kasar Kamaru da ci 4 ba ko daya a karawar da suka yi a Najeriya ranar Sallah.
An gudanar da wasan a filin wasa na Uyo, da ke jihar Akwa Ibom.
Wasan ya samu halartar dukkan wani mai ruwa da tsaki a cikin harkar kwallon kafa a Nijeriya. Ministan Wasanni da Harkokin Matasa, Solomon Dalung ne babban bako.
Babban filin wasan na zamani, ya zama ba masaka tsinke inda masu sha’awar kallo su ka cika shi fal. Masu sharhin wasa sun ce Najeriya ta shafe shekaru da dama ba ta nuna irin bajintar da ta nuna kamar wannan karo ba.
Irin yadda zaratan ‘yan wasa irin su Mikel Obi, Kelechi Emenacho da Victor Moses su ka rika suburbuda tare da yin wasan kura da ‘yan wasan Kamaru, ya burge ‘yan kallo bugu da kari kuma ga shi kuma ranar ce ranar shagulgulan Babbar Sallah, sai ya kasance wasan ya zame wa masu kallo a talbijin cikin fadin kasar nan murna biyu kenan.
Najeriya da Kamaru dai su na cikin rukuni daya ne, inda a rukunin za a fidda kungiya daya tal a zaman daya daga sauran kungiyoyi biyar da za su wakilci Afrika a Gasar Cin Kofin Duniya na 2018.
Najeriya ta yi nasara a kan wasanni uku da ta kafsa, kuma ita ta daya a rukunin su.
Discussion about this post