KWALARA: Mutane 7 sun rasa rayukansu a sansanin yan gudun hijira dake Barno

0

Jami’a a Kungiyar MSF Anna Cillers ta ce akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sanadiyyar bullowar cutar kwalara a wasu sansanonin yan gudun hijra dake Maiduguri, jihar Borno.

Anna Cillers ta ce a yanzu haka mutane 200 ne ke samun kula a cibiyoyin kiwon lafiya dake sansanonin Dala da Muna.

Ta ce mutane bakwai din da suka mutu daga sansanin Muna suke.

Ta ce rashin tsaftace muhali musamman abinci da ambaliyar ruwan da akayi a jihar ne yayi sanadiyyar yaduwar cutar.

Ta ce wasu hanyoyi da su dauka domin hana yaduwar cutar sun hada da samar da wuraren samar da ruwan sha da suka tsaftace shi da sinadarin ‘Chlorine’, karo gadajen kwanciya 40 a asibitocin dake sansanin da kuma maganin ‘Rehydration Therapy’.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Haruna Mahalia ya ce sun sanar da masu unguwanin jihar da su wayar da kan mutane akan mahimmancin tsaftace muhalli saboda rigakafi daga kamuwa da cutar.

Share.

game da Author