Kungiyar manyan ma’aikata, kungiyar ma’aikatan kimiya da fasaha da kungiyar ma’aikatan jami’ar (Ba malamai ba) na jami’ar Kaduna (KASU) sun fara yajin aikin ranar Litini.
Shugaban kungiyar manyar ma’aikatan jami’ar Kantoma Bala ya sanar da haka da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya inda ya kara da cewa kungiyoyin guda uku sun hadu ne a matsayin ‘Joint Action Committee JAC’ domin shiga yajin aikin.
Ya ce kungiyoyin ma’aikatan jami’ar sun amince da su shiga yajin aikin ne saboda rashin aiki da yarjejeniyar shekara 2009 da gwamnatin tarayya ta ki cikawa.
Sauran dalilan sun hada da;
1. Rashin biyan ma’aikata cikakken albashinsu a lokacin da ya kamata.
2. Rashin kayayyakin aiki uasamman a fannin koyar da dalibai.
3. Rashin kammala wasu ayyuka da gwamnatin ta fara yi wanda har yanzu bata gama ba.