Kungiyoyin ma’aikatan jinya da unguwar zoma NANNM, hadadiyar kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya da gamaiyar kungiyoyin kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya JOHESU sun fara yajin aiki gama gari yau Laraba.
Shugaban kungiyar NANNM Abdurafiu Adeniji ya sanar da hakan ranar Talata kuma yana kira ga duk ma’aikatan jinya da su amsa kiran kungiyar.
Idan ba a manta ba kungiyoyin ma’aikatan jinya sun bada wa’adin kwanaki 7 wa gwamnati don ta biya alkawurran da ta dauka wa ma’aikatan tun a shekaran 2012.
Abdrafiu Adeniji ya ce bukatun ma’aikatan jinyan ya hada da; rashin biyan ma’aikatan alawus, rashin kara wa ma’aikatan da suka cancanci karin girma a wurin aikinsu da sauransu.
Bayan haka ministan kiwon lafiya ya roki alfarman kungiyoyin ma’aikatan jinya da kada su gudanar da yajin aikin.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tattaunawa da shugabanin kungiyoyin domin kawo karshen rashin jituwan.