Wata kungiya mai jajircewa wajen kare hakkin ‘yan jarida, ta caccaki kasar Kamaru bisa yawan take hakki da ‘yancin ‘yan jaridu da ta ke yi na daure su. Kungiyar da aka fi sani da CPJ, ta nemi Kamaru ta sako dukkan ‘yan jaridar da ta tsare ba tare da gindaya musu sharudda ba.
Musamman, ita CPJ ta nuna damuwar ta sosai kan ci gaba da tsare wani dan jarida, wanda dan Najeriya ne a kasar Kamaru.
Ahmed Abba, wakilin Sashen Hausa na Radiyo France International, ya na tsare a Kamaru. An kama shi ne yayin da ya ke tattara bayanai da rahotanni kan ta’addancin Boko Haram. Ita dai Kamaru, ta zargi Abba ne da kutsawa neman bayanai ba bisa izni ba.
Rahoton da CPJ ta fitar ya fito karara ya kushe Kamaru, dangane da yadda ta ke garkame da’yan jaridu a karkashin Dokar Dakile Ta’addanci ta 2014. A kan haka ne kungiyar ta ce Kamaru na gallaza wa ‘yan jaridu da kuma yi musu takunkumi a karkashin wannan doka.
Sai dai CPJ ta yi kira da babbar murya ga Hukumar Shirya Gasar Kwallo ta Afrika, da ta kwace damar daukar nauyin Gasar Cin Kofin Afrika na 2019 da za a gudanar a Kamaru. CPJ ta yi rokon cewa kada a amince da Kamaru har sai ta sako dukkan ‘yan jaridun da ke daure a kasar tukunna.