Kungiyar likitoci masu aikin jinkai MSF ta ce a watan da ta gabata mutane 2,627 sun kamu da cutar kwalara sannan 48 daga cikin su sun rasa rayukansu sanadiyyar cutar a jihar Borno.
Wata Jami’a a Kungiyar Anna Cilliers ta ce a Maiduguri mutane 1,425 ne suka kamu da cutar, Dikwa kuwa tana da mutane 600 sannan Monguno na da mutane 602.
Ta ce kungiyar su na iya kokarinta wajen ganin sun rage yaduwar cutar musamman a kananan hukumomin Monguno da Dikwa ta hanyar bude asibitin kula da mutanen da suka kamu da cutar dake da yawan gadaje 100 a Dala.
Anna Cilliers ta ce ranar 16 ga watan Agusta kungiyar ta kula da mutane 491 wanda suka kamu da cutar amma ta ce sun sallami mutane 475 domin sun sami sauki.