Kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ta yi kira ga malaman jami’o’i da su koma bakin aiki daga gobe Talata.
Kungiyar ta sanar da haka bayan kammala taron da ta yi da ministan kwadugu, Chris Ngige.
Kungiyar ta ce kowani malami ya koma aiki daga gobe sannan kuma zata saurari gwamnatin tarayya zuwa watan Oktoba don cika alkawuran da ta dauka.