Kungiyar Kwadago za ta kwance wa gwamnoni masu taurin biyan albashi zani a kasuwa

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta bayyana sunaye tare da kunyata gwamnonin da su ka rike albashin ma’aikata tare da kudaden fanshon su, wata da watanni ba su biya su ba.

Kungiyar ta ce za su yi wa kowane gwamna wannan tonon silili ne a jihar sa.

Ta kuma kara da cewa a cikin watan Agusta da ya wuce, bayan tashi daga wani taro da kwamitin aiwatarwa na kungiyar a Abuja, sun bayyana wannan matsala da cewa abin kunya ne, duk da irin bilyoyin kudaden da gwamnatin tarayya ta rika bai wa jihohi a matsayin kudaden toshe baraka, har yau jihohi da dama sun kasa biyan ma’aikata albashi da kudaden fanshon su na tsawon wata da watanni.

Kungiyar ta bayyana jihohi irin su Kogi, Benuwai da Bayelsa a matsayin babban misali na jihohin da ma’aikata ke bin bashin albashi da kudaden fansho na watanni biyar zuwa goma.

“Akwai wasu jihohin irin su Kaduna da Zamfara, wadanda sun ki su bayyana irin yadda suka kashe kudaden toshe barakar da gwamnatin tarayya ta rika dumbuza musu, dga kudaden biyan Paris Club. Sun ki su bayyana wa jama’a duk kuwa da irin neman su bayyana da kungiyoyi da sauran jama’a su ka rika yi.” Inji Ayuba Wabba, Shugaban Kungiyar da kuma Sakataren Peter OZO-Eson.

Kungiyar ta kuma ce za ta rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasika, domin ta nemi ya tilasta wa wadannan gwamnoni su fito su bayyana yadda suka kashe bilyoyin kudaden da ya ba su.

Share.

game da Author