Kotu ta sa ranar yanke hukuncin dakatar da Sanata Ndume

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanar da ranar 13 Ga Oktoba ranar da za ta yanke hukuncin karar da Sanata Ndume ya kai dangane da dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi masa.

Mai Shari’a Babatunde Quadri ne ya fadi haka inda ya ce ranar ne zai zartar da hukuncin cancanta ko rashin cancantar dakatar da Ndume da aka yi.

Lauyan Sanatan na Barno ta Kudu, mai suna Marcel Oru, ya nemi kotun ta haramta dakatarwar saboda ya ce an yi ta ne ba bisa ka’ida ba, zalunci ne kuma babu wani dalilin yin hakan.

Ya ce zargin da majalisa ta kafa hujja da shi har aka dakatar da wanda ya ke karewa tsawon watanni shida, ba su kai dalilai na dakatar da mamba na Majalisar Dattawa ba.

An dakatar da Ndume ne tun a ranar 30 Ga Maris, sakamakon ikirarin da aka ce ya yi, inda ya nemi majalisa ta yi bincike kan wasu motocin da kwastan su ka kama.

Motocin dai an shigo da su ba bisa ka’ida ba, kuma aka alakanta wata motar cewa ta Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ce.

Share.

game da Author