Kotu ta daure wani magidanci da ta kama da laifin aikata lalata da ‘yar cikinsa

0

Kotun sauraron kararraki dake Ado Ekiti ta daure wani magidanci mai suna Adeyanju Basiri dan shekara 55 da ta kama da laifin aikata lalata da ‘yar cikinsa.

‘Yar sandar da ta shigar da karar, Monica Ikebulo ta ce Adeyanyu ya yi lalata da ‘yarsa ne mai shekara 7 ranar 11 ga watan Satumba a Ado-Ekiti.

Ta ce mahaifin yariyar da bokansa wanda ya gudu sun so su yi tsafi ne da yarinyar.

Adeyanyu ya fada wa kotun cewa ya kwana da ‘yarsa sau tara sannan a duk lokacin da ya gama amfani da ita yakan share gabanta da wani farin kyalle.

Daga karshe alkalin kotun Dolapo Akosile ya dakatar da sauraron karan zuwa 12 ga watan Oktoba domin samun shawarwari.

Share.

game da Author