Kotu ta ba Gwamnatin Tarayya iznin haramta Kungiyar ‘Yan Biafra

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bai wa Gwamnatin Tarayya damar haramta kungiyar ‘yan taratsin kafa Biafra, wato IPOB .

Babban Alkalin Najeriya mai rikon kwarya, Abdul Kafarati ne ya bayar da iznin a ranar Laraba. Hakan ya biyo bayan wasikar da Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wa Babbar Kotun ce, inda ya nemi ta ba shi iznin haramta kungiyar.

Gwamnonin Kudu-maso-Gabas ne su ka fara haramta ta, daga bisani kuma Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana kungiyar da sunan ‘yan ta’adda.

Buhari ya rubuta takardar neman iznin haramta IPOB ne zuwa kotu, biyo bayan wasu kalamai da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yi cewa Gwamnoni da sojoji ba su da ikon haramta IPOB. Kalaman na Saraki dai sun kawo masa tsangwama da bakin jini a fadin kasar nan.

Share.

game da Author