Kotin Koli ta kori dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Vandeikiya/Konshisha jihar Benue Hermen Hembe daga kujerarsa a majalisar wakilai.
Dan majalisan ya daukaka kara ne bayan kotun daukaka kara ta amince da soke zabensa da kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Benue ta yi.
Bayan haka a hukuncin da kotun kolin ta yanke, ta umurci Herman Hembe da ya maido da kudaden da aka biya shi a matsayin dan majalisa tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu.
Kotun ta umurci Hermen da ya biuya taran naira miliyan daya.