Ko Buhari ya fito takara a 2019, Atiku zan yi muddun ya fito takara –Aisha Alhassan

0

Ministan ayyukan mata Aisha Jummai Alhassan ta ce zai zamo munafunci idan har bata yi tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ba a zaben 2019 muddun ya fito takara.

Ta ce hakan zai zamo munafunci ganin cewa shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san irin kusancin ta da Atiku Abubakar.

Aisha Alhassan ta fadi haka ne da take hira da gidan jaridar BBC Hausa wajen mai da martini ga yayada ta da akeyi wai tana yi wa Atiku kamfen bayan tana gwamnatin Buhari.

“ Mai girma Atiku Uban daki na ne, tun kafin in shiga siyasa, sannan bayan na shiga siyasa kuma ya zama uban daki na a siyasa. Sannan Baba Buhari bai ce zai tsaya takara a 2019 ba sannan ina tabbatar maka idan Baba ya ce zai yi takara a 2019, zan je in durkusa a gaban Baba in ce mishi Baba nagode da ka bani daman yin aiki a karkashin ka a matsayin minista. Amma Baba kamar yadda ka sani Atiku ne uban daki na, in fa yace zai tsaya takara don bai ce zai tsaya ba.”

Aisha ta ce abinda ya sa ta yi masa kirari da shugaban kasa a 2019 shine don suna sa ran zai tsaya takara.

Bayan Haka kuma ministan tace tun daga fadin wannan magana da tayi a ziyarar da suka kai wa Atiku ake ta yada ta har wasu na cewa wai Buhari zai Kore ta da ga aiki.

Ministan tace bata tsoron haka sannan ta tabbatar Buhari bazai kore ta ba don ta fadi haka sai dai idan wani laifin tayi.

Ta ce Allah ne ya bata minister kuma idan ma an koret a lokacinta ne yayi.

Share.

game da Author