Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun koka akan yawan mutuwan yara da mata da Najeriya ke samu.
Ma’aikatan kiwon lafiya ta fadi haka ne bayan rahotan yawan mutuwan yara da mata da kungiyar WHO, Asusun UNFPA da Asusun UNICEF suka bada a taron wayar da kan mutane kan illolin rashin samun ingantacciyar kiwon lafiya da ya gudana a kwalejin koyar da aikin likitanci dake jihar Legas.
A jawabin ta babban bakuwa a taron Olusola Odujinrin yayin ta ce har yanzu akwai sauran rina a kaba domin dole sai Najeriya ta kara maida hankali kan inganta fannin kiwon lafiya kafin a kai ga ci.
Ta kuma kara da cewa rahotan ya nuna cewa Najeriya na da kashi 15 bisa 100 wajan karin yawan mutuwan da ake samu a kasar amma tace hakan zai iya zama labari idan aka mai da hankali wajen kau da wannan matsala.
Bayan haka Odujinrin ta ce daya daga cikin matsalolin da ke gurgunta fannin kiwon lafiya musamman cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko shine karancin kudi.
” Har yanzu ana matukar fama da rashin kudi a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, wanda hakan yakan sa kaga har ta kayayyakin aiki a asibitocin sun kare kaf ko kuma basu ma kwata-kwata.
Discussion about this post