Kira da a maida shirin inshorar lafiya dole ga kowani dan kasa- Attahiru Ibrahim

0

Shugaban riko na hukumar inshoran kiwon lafiya na kasa NHIS Attahiru Ibrahim ya ce kamata ya yi kowani dan Najeriya ya zamana yana cikin shirin inshorar kiwon lafiya.

Ya ce hakan zai taimaka wa gwamnatin wajen samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga mutanen kasan baki daya.

Attahiru Ibrahim ya ce hakan zai yiwu ne idan gwamnati ta gyara dokar kafa hukumar inshoran lafiya din.

Ya ce hukumar za ta hukunta duk ma’aikacin inshoran da takama da laifin cin hanci da rashawa.

Share.

game da Author