Kauyuka 66 ne ke fama da matsalar ambaliyar ruwa a jihar Neja

0

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Neja NSEMA Garba Shehu ya ce kauyuka 66 a karamar hukumar Makowa na fama da matsalar ambaliyar ruwa.

Garba sanar da haka ne da yake zantawa da kamfanin dillanci labaran Najeriya a Minna ranar Laraba inda ya kara da cewa ambaliyar ta lashe gidaje, gonaki da dabbobi da dama a kauyukan.

Ya ce ruwan saman da aka yi a ranar Talata kamar da bakin kwarya ne ta yi sanadiyyar ambaliyar da ya hada da kauyen Ketso kauyen mataimakin gwamnan jihar Ahmed Ketso.

Garba Salihu ya ce sun ziyarci kauyukan domin gani wa idanuwarsu irin hasarar da mutane su ka yi.

Share.

game da Author