Kwamishinan kula da kananan hukumomi da aiyukkan sarakunan gargajiya na jihar Nasarawa Haruna Osegba yace kashi 60 bisa 100 na ma’aikatan kananan hukumomin jihar na karban albashi kowace karshen wata batare da sun tsinana komai ba a wurin aikin su.
Ya sannar da haka ne da yake zantawa da wakilan kungiyar ma’aikatan jarida NUJ inda ya kara da cewa gwamnati za ta samar da shiri don kawar da irin haka a tsakanin ma’aikatan jihar.
Haruna Osagbe ya ce gwamnatin na nuna takicinta akan yadda ma’aikatan kananan hukumomin ke karban albashi ba tare da sun tsinana komai ba a wurin aiki.
Ya ce saboda hakan ne gwamnatin za ta kara wa duk ma’aikatan da ke nuna hazaka a aikin su don karfafa musu guiwa bayan ta kammala tattance sunyen ma’aikatan da suka cancanci hakan.
Ya kuma tabbatar da cewa za su biya ma’aikatan kananan hukumomin cikakken albashin su yadda ya kamata bayan ta kammala tattancesu.
Daga karshe wakilan kungiyar NUJ Suleman Abubakar ya yi kira ga kwamishinan da ya tabbatar bayan sun kammala tattancewan ma’aikatan kanana hukumomin za su sami cikakken albashinsu kamar yadda yayi alkawari.
Discussion about this post