Kamfanin NNPC ya koma neman danyen man fetur a Sokoto

0

Watanni kadan bayan da Boko Haram su ka yi wa ma’aikatan NNPC kwanton bauna har suka kashe wasu malaman jami’ar Maidurguri a Tafkin Chadi, hukumar ta sake tura wata tawagar domin aikin hako danyen man fetur a yankin madatsun Sokoto, wato Sokoto basin.

Babban Manajan Daraktan Hukumar NNPC, Maikanti Baru, ya bayyana wa Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal haka a yau Laraba, lokacin da gwamnan ya kai ziyara hedikwatar hukumar a Abuja.

Baru ya ce har ila yau NNPC na nan kan bakan sa na ganin an samu danyen man fetur a Arewa.

“Mun dade a kan wannan batu, na kokarin ganin an samu danyen man fetur a Arewa, kuma mun fara daukar matakai, domin tuni mun sayo na’urar gwaji wadda a yanzu ana kan nazari da auna ta domin gano irin albarkatun kasar da ke kwance a karkashin kasar a yankin.” Inji Baru.

“Mun kuma bayar da kwangilar ganowa tare da shata mana murabba’in yankin da za mu yi aikin neman danyen mai. Ina kuma farin cikin shaida maka cewa tuni mun kwakulo samfur kuma an yi nazarin yadda za a fara aikin hakan domin a yi kokarin samowa.” Inji shugaban na NNPC.

Share.

game da Author