Kalubale 7 da Atiku ya yi wa masu ce masa barawo

0

A kokarin sa na karyata zagin wawurar dukiyar kasar nan da yawancin ‘yan Najeriya ke yi masa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai taba satar ko kwabo daga dukiyar al’umma ba, a tsawon shekarun da ya yi a gwamnati.

Ana dai da tabbacin cewa Atiku ya dade ya na harin kujerar shugabancin kasar nan, kuma a 2019 ma zai sake jaraba sa’a.

A yayin da ya ke kewayen gani-da-ido na sabon ofishin kamfanin buga takardu na Yaliam Press Limited, wanda aka bude a unguwar Jabi, Abuja, Atiku ya ce dukkan arzikin da ake ganin sa da shi, ya samu ne ta hanyar jajircewar da ya ke yi wajen neman na kan sa.

Ana kyautata zaton cewa Atiku na daya daga cikin hamshakan attajiran ‘yan siyasar kasar nan, kuma wanda ya bayar da dimbin gudummawar zunzurutun kudi wajen kamfen din Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015.

Kwanan nan dai Atiku ya tayar da kura a siyasar Najeriya, yayin da ya caccaki jam’iyya mai mulki, APC, inda ya zarge ta da yin watsi da shi, tare kuma da juya masa, bayan ya yi mata gagarimar gudummawar da ta sa jam’iyyar ta samu nasara a zaben shugaban kasa a 2015.

Kalubalen Atiku Ga ’Yan Najeriya

1. Matsalar ‘yan Najeriya ita ce, su a tunanin su, mutum ba zai iya gina kan sa ba, sai ya hada da kudin sata.

2. Abin bacin rai ne a rika amayar da zargin sata a kai na, alhali an kasa fitowa da hujja ko da guda daya wadda ta tabbatar da cewa na wawuri dukiya a lokacin da na ke aiki.

3. Mutane masu dakusassar kwakwalwar rashin tunanin kirkiro dabarun kasuwanci, su a ko yaushe gani su ke yi kowa ma barawo ne kamar su.

4. Idan har Atiku barawo ne saboda kallon irin dimbin kasuwancin da ya ke yi da dukiyar sa, to ina so abokan gabar siyasa ta su fito su shaida wa ‘yan Najeriya su na su hanyoyin da su ka bi su ka mallaki bimbin dukiyar.

5. Ina kalubalantar duk wani wanda ke da wata hujja ko hujjoji cewa na wawuri dukiyar kasar nan, to kada ya rufa min asiri, ya fito ya tona ni.

6. Idan na zama shugaban kasa, ina da tabbacin cewa zan bai wa kowa mamaki, saboda na yi imani cewa zan yaki da cin hanci da rashawa fiye da yadda kowa ma ya taba yi a baya.

7. Duk da makarkashiya da algungumancin da ake kitsawa don a danganta ni da harkallar William Jefferson a Amurka, an yi shari’ar kuma an kammala tun a 2009, amma ba a kama ni da laifin komai ba.

Share.

game da Author