Kalaman nuna kiyayya ne su ka haddasa Yakin Basasa – Jibril Aminu

0

Tsohon Minista Jibril Aminu ya bayyana cewa kalaman kiyayya da kuma labaran zuki-ta-malle tsakanin harkokin siyasa, su ne su ka haddasa barkewar yakin Basasa a Nijeriya a cikin 1967.

Ya yi wannan jawabin ne a Kano, tare da Ministan Yada Labarai a wurin taron Kwararru Kan Harkokin Sadarwa.

Aminu ya kara da cewa ya zama wajibi mu yi taka-tsantsan da dukkan wasu abubuwan da za su iya jefa kasar nan fadawa cikin rikicin da ka iya haddasa sake barkewar wani sabon Yakin Basasa a kasar nan.

Ya kuma ja kunnen kafafen yada labarai da su guji buga labaran da ka iya haifar da rabuwar kasar nan.

Tun da farko, ministan yada labarai ya ce gwamnati ta damu da irin yadda ake yada kalaman kiyayya tsakanin jama’a, kungiyoyi da daidaikun mutane.

Ya ce gwamnati na kan hanyar magance labaran karya, kalaman kiyayya da haddasa fitintinu. Sai dai ya kara da cewa ba ya na nufin za a yi wa kafafen yada labarai takunkumi ba ne.

Share.

game da Author