Mutane shida sun rasa rayukansu sanadiyyar kifewar jirgin ruwa a rafin Benue da ya ketara ta karamar hukumar Gassol jihar Taraba.
Shugaban karamar hukumar Gassol Yahuza Yayau ne ya sanar da haka inda yace jirgin ya kife ne da ya ci karo da marmara a cikin ruwan. Ya ce sai da jirgin ta rabe biyu amma kuma har yanzu ba a san yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar hatsarin sai dai an san cewa mafi yawan su manoma ne daga kauyen Mutum Biyu.
Yahuza Yayau yace wasu ma’aikatan su sun tsamo gawawwakin mutane 6 daga cikin sannan har yanzu ana neman sauran mutanen.
Ya kuma kara da cewa mai yiwuwane gawanwakin mutanen ya karu.