Gwamantin jihar Kebbi ta sanar da cewa yara 656 sun kamu da cutar Kenda a kananan hukumomi 21 na jihar.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Mannir Jega ya sanar da haka inda ya kara da cewa hakan ya faru ne saboda mazaunan jihar musamman iyaye mata sun ki yi wa ya’yansu alluran rigakafin cutar tun a shekaran 2016.
Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya na jihar Usman Kambaza ya ce za su aika da ma’aikata 1,131lungu-lungu a jihar domin yi wa yara alluran rigakafin cutar.
“Za mu shawo kan cutar ta hanyar yi wa yara 898,174 alluran rigakafi a jihar.
“Yara ‘yan watani 9 zuwa shekaru 5 za a yi wa alluran rigakafin a mazaba 225.”
Daga karshe Usman Kambaza ya yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabanin addini, gidajen jaridu da masu ruwa da tsaki a jihar da su taimaka da wayar da kan mutanen jihar musamman iyaye mata don asami nasara a aikin.