Jami’an tsaro sun harbe wasu daga cikin maharan kauyen Ancha, jihar Filato

0

Jami’an tsaro na Soji ta sanar da kisan wasu mutanen biyar daga cikin wadanda ake zargi sune suka nemi tada zaune tsaye a kauyen Ancha dake jihar Filato.

Idan ba a manta ba a cikin kwanakin da suka gabata gidan jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa wasu mutane sun kai hari a kauyen Ancha inda mutanen 19 suka rasa rayukansu.

Mazauna kauyen sun ce suna zargin wasu makiyaya ne dake zama a yankin tare da su suka kai musu harin.

Shugaban jami’an tsaron ‘Operation Safe Haven’ Adamu Umar ya ce sun harbe mutanen biyar sannan wasu daga cikin maharan sun sami rauni.

Adamu Umar ya ce ma’aikacin su daya ne kadai ya sami rauni a lokacin da suka yi arangama da maharan sannan ma’aikatan su na nan na gudanar da fataro dare da rana a yankin domin farautar sauran maharan.

Bayan haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da aka kai a kauyen Ancha.

Share.

game da Author