Jami’an Kwastam sun kama motar Dangote make da naman Kaji

0

Hukumar kwastam ta kama motar Dangote dankare da naman kaza wanda gwamnati ta hana shigowa da su kasar a iyakar jihar Ogun.

Shugaban hukumar dake jihar Sani Magudu ya sanar da haka ranar Litini da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce motar na dauke da katan din kaji 3000 wanda ya kai Naira miliyan 47.

Sani Magudu yace sun sami labarin cewa akan shigo da kajin da aka hana shigowa da su Najeriya daga kasar Benin wanda hakan ya sa suka dana tarkon kama wadanda ke yin hakan.

Ya ce sun fara bin motar dake da lambar rajista ICT-13E-047 tun a wurin da suke lodi sannan suka sami nasaran kamata a hanyar Sagamu –Abeokuta ranar 16 ga watan Satumba da misalin karfe 3:45 na asuba.

Ya ce sun kama yaron motan amma direban ya tsere.

A yanayin da ake Sani Magudu y ace hukumarsu ta fara birne kajin sannan ya tabbatar da cewa za su yi kokarin kama direban motar.

Share.

game da Author