Hamshakin dan kasuwannan wanda ya fi kowani bakin mutum arziki a duniya, Aliko Dangote ya ce yana fatan farashin danyen mai ya ci gaba da fadi zuwa dan wani lokaci saboda kasashen da suke tasowa da dogaro da mai su nemo wasu hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasashensu da samun kudaden shiga.
Dangote ya fadi haka ne a taron jiga-jigan ‘yan kasuwa musamman na kasashen Afrika da aka shirya a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana yanzu.
Dangote yace dole ne kasashe musamman na Afrika su farfado daga bacci sannan su karkata akalar su zuwa ga nemo wasu hanyoyin da zasu dinga samun kudaden shiga ba dogaro da danyen mai ba.
Shugaban Kasar Rwanda Paul Kagame shima ya tofa albarkacin bakinsa a wajen tattaunawar in da yace dole ne kasashen Afrika su maida hankali wajen ilmantar da matasa da bunkasa fannin ilimi a kasashensu.
Kagame yace yin haka ne zai taimaka wajen samar da matasa masu ilimin da za su fadada fannin kasuwanci da zuba jari a nahiyar daga yanzu har zuwa gaba.