Wani mai buga fosta ya bayyana a gaban alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, inda ya bayar da shaidar cewa ya na bin Kwamitin Tazarcen Goodluck Jonathan bashin kudi naira miliyan 24, a matsayin sauran cikon kudin da har yau ba su ba shi ba, daga aikin buga fostar 2015 da ya yi musu.
Shugaban kamfanin buga takardu na ‘Paste Poster Company Limited’, Olusegun Idowu ne ya bayyana haka ranar Labara a kotun da ke Lagos.
Daraktan Yada Labaran Tazarcen Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode na daga cikin wadanda ake tuhuma dangane da salwantar naira biliyan 4.9 da aka karkatar cikin asusun kamfen din.
Sauran wadanda ake tuhumar a gaban alkali Rilwan Aikawa, sun hada da tsohuwar Karamar Ministar Kudi, Nenadi Usman, da kuma Danjuma Yusuf sai kuma ‘Joint Trust Limited’.
An zargin su ne da aikta laifuka har 17, wadanda su ka hada makarkashiya, mallakar kudin sata da kuma harkalla.
Idowo, wanda EFCC ce ta gabatar da shi a matsayin shaidar ta, ya bayyana wa kotu cewa aikin buga fosta na naira miliyan 54 ya yi musu, amma an ba shi miliyan 30 a tsitstsinke, yanzu saura naira miliyan 24 ya ke bi.
Za a ci gaba da shari’a ranar 22 Ga Nuwamba, 2017.