Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta tallafawa wasu yara 60 mazauna garin Daura domin samun ilimin Boko.
Aisha ta sanar da haka ne ranar Litinin din da ya wuce a garin Daura.
Ta ce ilimantar da yara zai taimaka wajen kawo ci gaba a kasarnan sannan ta yi kira ga masu kudi da su rika tallafawa yaran da basu da halin samun irin wannan ilimi na zamani domin samun ci gaba a kasa.
Bayan haka, Uwargidan shugaban kasa ta raba kayayyakin abinci ga marasa hali da zaurawa a garin Daura.
Aisha Buhari ta kira ga iyaye da su maida hankali wajen ba ya’yansu ilimin zamani musamman mata.
Sarkin Daura Umar Faruk da matar gwamnan jihar Zakiyya sun yaba wa wa Aisha Buhari da irin wannan kokari da tayi wa marayu da matan yankin.
Bayan haka Aisha Buhari ta ziyarci dakin kula da mata marasa lafiya da take gina wa a asibitin Daura wanda aka fara tun a Mayu.