Fitaccen lauya Femi Falana, ya ragargaji Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN dangane da kukan da ta yi cewa lamunin kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta bayar ba tare da ruwa ba, wato tsarin tasirifun kudi ta halastacciyar hanya da a Musulunce a ke kira ‘SUKUK.’
A karshen makon jiya ne dai CAN ta ce tsarin wata makarkashiyar musuluntar da Najeriya ce gaba dayan ta.
Gwamnatin Tarayya dai ta ce za ta fito da takardar lamunin har na naira biliyan 100, ta raba a tsarin tasrifi a musulunce, na Sukuk.
A kan haka ne Falana ya yi bayani a wani taron masana tattalin arziki na SERAP a Lagos.
Falana ya ce Sukuk halastacciyar hanya ce da gwamnati za ta samu kudade ba tare da tatse aljihunan jama’a da sunan haraji ko kudin ruwa ba.
“Wannan tsari fa a duk kasashen duniya da su ka ci gaba wadanda ba ma na Musulunci ba ne, shi su ke rububin yi, kuma jama’a sun karbe shi hannu bibbiyu.”
Sai Falana ya ce idan har CAN ta ji haushi, to ita ma ta fito da na ta tsarin na Sukuk din wanda ba zai kuntata wa al’umma ba.
Daga nan sai ya kara ragargazar shugabannin addinai masu amfani da rigar kungiyar addini su na raba kan jama’ar kasar nan, ya na mai cewa irin wadannan malaman addinin ba taimaka wa kasa su ke yi ba, sai ma neman rikita ta kawai.