Haramta kungiyar Biafra ba daidai bane, kuma ba za mu yarda da haka ba – Inji Saraki

2

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewa gwamnonin Kudu-maso-gabas da kuma rundunar sojojin kasar nan, basu da ikon da za su haramta kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu, mai hankoron kada Biafra.

Saraki ya yi wannan bayanin ne a wani jawabi da ya fitar yau in da a ka wallafa ya shafinsa na sada zumunta.

Saraki ya ce gwamnonin da kuma hukumar tsaro ta sojoji ba su bi ka’idar da ta dace ba, kafin su haramta kungiyar.

“Akwai inda dokar kasar nan ta nuna cewa duk kungiyar da aka soke ko kuma aka haramta ta, ba tare da bin wasu ka’idoji na doka ba, ta na nan daram, ba ta soku kuma ba ta haramtu ba.

“Na tabbatar shugaban kasa zai yi abin da ya san shi ya fi dacewa, wato bin matakin da doka ta shimfida, kafin a soke ko haramta IPOB. Don haka duk wani mai ja-in-ja, to ya kwantar da hankalin sa, domin za mu bi kadin rikicin kuma mu yi kwakkwaran bincike.

Share.

game da Author

  • Abdulmumini Bala Gobbiya

    Saraki kaji tsoron Allah kayi adalchi wa ratukan da suka salwanta saka makon da rikichin ya haifar a nigeria.

  • Bapetel M Adamu

    Idan har za abar ipob soyi abunda suna so ta lallai fitina bazai kare akasan nanba. Allah kare.