Tsohuwar ministan sufirin jiragen sama, sanata Stella Oduah, ta ce har yanzu jam’iyyar PDP bata daddara da irin matsalolin da ta fada ciki ba wanda yayi sanadiyyar faduwar ta zabe a shekarun baya.
Stella ta ce ba a bi dokar jam’iyyar ba a zaben fidda dan takarar gwamnan jihar Anambra da jam’iyyar ta gudanar a jihar makon da ya gaba.
” Na rubuta wa Uwar jam’iyyar wasikar mika kuka ta kan yadda a ka gudanar da zaben fidda dan takaran domin a sake dubawa amma har yanzu ba su ce mini komai akai ba.
Stellah wanda ita ma tayi takaran a zaben fidda dan takaran gwamna na jam’iyyar PDP ta kara da cewa idan har ba a duba matsalolin da aka fuskanta a wannan zabe ba to har yanzu fa jam’iyyar ba ta yi shirin gyara kurakuran da ta yi a da ba.